Kotu Ta Yankewa Jarumi Salman Khan Zaman Gidan Yari Na Tsawon Shekaru Biyar - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Kotu Ta Yankewa Jarumi Salman Khan Zaman Gidan Yari Na Tsawon Shekaru Biyar


    Wata Kotu a Kasar Indiya ta yankewa shahararen jarumin finan-finan Indiya Salman Khan hukuncin zaman shekaru biyar a gidan yari saboda laifin kashe wasu dabbobi wadanda basu da yawa a duniya a wata farauta da yayi.

    Lauya mai shigar da kara, Mahipal Bishnoi ya shaidawa manema labarai a birnin Rajasthan da ke Jodhpur cewa: "Kotu ta yanke ma Salman Khan hukuncin shekaru biyar a gidan yari da kuma tarar rupees 10,000 ($150)."

    Kotu ta yankewa shahararen jarumin Bollywood shekara 5 a gidan yari
     Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Lauyan ya cigaba da cewa a yanzu ana shirye-shiryen kama jarumin mai shekaru 52 a duniya don tisa keyar sa zuwa gidan yari na garin Jodhpur.

    Sai dai Salman Khan ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa dashi kuma yana da damar daukaka kara a wata kotun.

    No comments