Selfie A Masallacin Ka,a Na Iya Bata Aikin Hajji
'Selfie’ na iya rusa Hajji – Limamin Ka’aba
Limamin masallacin Ka’aba, Faisal Ghazzawi ya
bukaci mahajjata da su kaucewa daukar hotunan
‘selfie’ don gudun kar su bata aikin Hajjinsu.
Faisal Ghazzawi ya yi wannan kiran ne a hudubar da
ya gabatar ta sallar Juma’a a ranar Sallah Babba.
Ya ce wasu mahajjatan kan dauki hotuna ne don
sanar da al’umma cewa su na aikin Hajji da kuma
fatan in sun koma gida a ce da su Alhaji ko Hajiya.
Hakan, in ji limamin zai iya kore ikhlasi daga cikin
niyyarsu tare da haddasa riya, abubuwan da za su
iya bata Hajji dungurungum.
fLimamin Ka’aba, Faisal Ghazzawi
Jigon hudubar dai shi ne darussan da Hajji ke
koyarwa al’ummar Musulmi.
Daga cikin darussan da limamin ya zayyana akwai
hadin kai, da kadaita Allah cikin bauta da addu’a da
kuma neman taimako.

No comments