Haryanzu Ban Cire Rai Da Dawowa Harkan Film Ba Inji Zainab Indomie - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Haryanzu Ban Cire Rai Da Dawowa Harkan Film Ba Inji Zainab Indomie

    Har yanzu ban fidda ran dawowa harkar fim ba – Zainab Indomie

    Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood wadda aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa tana sa ran zata dawo harkar fim gadan-gadan ta kuma yi fice nan ba da dadewa ba.

    Shaharraiyar jarumar wadda a yanzu haka tauraruwar ta ta riga ta dishe ta bayyana cewa tana nan tana murmurewa tana kuma kara kammala shire-shiren ta domin ta dawo da karfin ta ta kuma disashe taurarin wasu jaruman a harkar yanzu.

    Majiyar mu, dai ta samu cewa a kwanakin baya anyi ta rade-raden cewa jarumar tana fama da wata matsanaciyar rashin lafiya ne da kuma ta ke hana ta walwala da harkokin nata kamar yadda ta saba.

    Haka ma dai a baya jarumar ta fito a kafafen sadarwar zamani inda tayi tofin Allah-tsine ta kuma sha alwashin yi wa duk wanda ya kara cewa tana fama da kanjamau Allah ya isa.

    No comments