Whatsapp Zai Fara Kama Admin Masu Rubuce-Rubucen Banza - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Whatsapp Zai Fara Kama Admin Masu Rubuce-Rubucen Banza

    An fara kama masu mugayen
    rubutu a shafin Whatsapp.

    An soma damke masu rubuce-rubuce a shafin
    sadarwar zamank na What’sapp a dokar wasu
    Kasashe ana iya kama wanda ya yada abin da
    bai dace ba
    A wata kasa an damke wani Saurayi da ke kula
    da wani zauren na What’sapp Mun samu labari
    cewa sai Jama’a sun bi a hankali don kuwa sai
    WhatsApp ya aika mutum kurkuku a yanzu a
    wasu kasashen.
    Sai a bi a hankali da WhatsApp A dokar wasu
    Kasashe irin su India dai ana kama mutane
    idan su ka yada mugun abu a kafafen sadarwa.
    Wanda za kuma a damke da laifi kuma shi ne
    mai kula da zauren a ko yaushe aka samu irin
    wannan matsala don a doka shi ya kyale aka
    rika yada wannan abu.
    A can wata kasa an kama wani mai suna
    Longton Jamil bisa zargi yada sakonni marasa
    kyau a shafin na Whatsapp inda shi kuma yace
    ya saba gargadin mutane a zauren na sa.
    Yanzu haka akwai wani Japeth Mulewa da yake
    hannun Hukuma a dalilin haka. Kwanaki ku ka
    ji cewa Sojoji sun fara bibiyar shafin gizo a
    Najeriya domin lura da abin da Jama’a ke
    yadawa.
    Yanzu haka Jama’a sun yi tir da wannan tsari
    su kace an koma mulkin Soja ne kurum da aka
    baro a can baya.

    No comments