Nigeria Ta Sayi Kayan Yaki Daga Hannu American - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Nigeria Ta Sayi Kayan Yaki Daga Hannu American

    A Karshe Amurka Ta Sayarwa Nijeriya Jiragen Yaki
    Da Makamai.

    Gwamnatin Amurka ta sayarwa Nijeriya jiragen yaki
    Samfurin Tucano A-29 har guda 12 da wasu
    makamai wadanda aka kiyasta kudadensu a kan
    dala milyan 593.
    Tuni dai, ma'aikatar tsaron Amurkan ta sanar da
    majalisar Tarayyar kasar game da sayar da
    makaman. Amurka dai ta kakabawa Nijeriya
    takunkumin hana sayar mata da makamai kuma a
    shekarar 2014, Tsohon Shugaban Amurka, Barack
    Obama ya ki amincewa da wata bukata na Shugaba
    Goodluck Jonathan na neman a sayarwa Nijeriya
    makamai don murkushe Boko Haram.

    No comments