Manyan Ayyuka Guda Biyar (5) Na Ranar Arfa Ga Wanda Baije Aikin Hajji Ba - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Manyan Ayyuka Guda Biyar (5) Na Ranar Arfa Ga Wanda Baije Aikin Hajji Ba



    MANYAN AIYUKA GUDA 5 NA RANAR ARFA GA WANDA BAI JE AIKIN HAJJI BA

    Daga Abu Abdirrahman Assalafy Kano

    Manyan aiyuka guda 5 da ake so mutum ya aikita a wannan Rana ga wanda bai sami damar zuwa aikin hajji ba.

    *1-Yawaita Addua*

    Mustahabbaine ga wanda baije aikin hajjiba ya yawaita addua da rokon Allah a wannan yini na ARFA,saboda fadin Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ;-
    *(Mafi alkhairi addua itace adduar ranar ARFA)*
    @ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺑﻪ ﺍﻟﺴﻠﺴﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ

    Fadin Manzon Allah s.a.w mafi alkhairin addua itace adduar ranar ARFA ya hada wanda yake aikin hajji da wanda yake gida bai je ba aikin hajji ba.

    *2-Yawaita Ambaton Allah mai yawa*

    Mafi alkhairi cikin ambaton Allah shine karatun Alqurani mai girma.
    Ana so mutum ya yawaita ambaton Allah mai yawa a wannan rana,saboda fadin Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ;
    *(.......Kuma mafi alkhairin abinda na fada a ranar ARFA ni da Annabawan da suka zo kafina shine:
    "ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ، ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ، ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ"*

    *"LÃ ILAHA ILLALLAH WAHDAHU LÃ SHARÎKA LAHU,LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WAHU ALA KULLI SHAI'IN QADEER"*
    @ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻓﻲ ﺳﻨﻨﻪ ﻋﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺷﻌﻴﺐ ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﻋﻦ ﺟﺪﻩ

    Kuma Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yana cewa;
    *(...........Ku yawaita Fadar LÃ ILAHA ILLALLAH,ALLAHU AKBAR,ALHAMDU LILLAH)*A kwanaki goma na farkon zul-hijja.
    @ﻭﺃﺧﺮﺝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ ﻓﻲ ﻣﺴﻨﺪﻩ.

    *3-Yawaita aiyukan alkhairi*
    Saboda fadin Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ :
    *(Babu wani yini da aiyukan alkhairi sukafi soyawa awajan Allah da girma a wajan Allah kamar aiyukan alkhairin a kwanaki goma na farkon watan zul-Hijja......)*
    @ﻭﺃﺧﺮﺝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ ﻓﻲ ﻣﺴﻨﺪﻩ.

    Manzon Allah s.a.w a wannan hadisin ya hade kwanakin guda goma kuma ranar ARFA tana cikinsu.

    *4-Yawaita Tuba da ISTIGHFARI da neman gafara domin ranace ta yanta bayi daga wuta zuwa aljanna,da kuma nisantar dukkan sabon Allah baki daya a wannan yinin*

    Saboda fadin Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ;
    *(Babu wani yini da Allah yake yanta bayinsa masu yawa daga wuta zuwa aljanna kamar yinin ranar ARFA)*
    @ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ.

    *5-Yin Azumi*

    Wanda baije aikin Hajji ba sunnane na Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yayi azumin Ranar AFRA.
    Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya kasance yana yin Azumin *ranar Tara ga watan Zul-hijjah,da ranar Ashura da kwanaki ukku a kowane wata*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﺑﺮﻗﻢ 2106. .

    *Falalar Azumin ranar Arfa ga wanda baije aikin Hajji ba*
    i-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
    *(Yin Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekara mai zuwa)*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3805.
    ii-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
    *(Duk wanda yayi Azumin ranar Arfa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekara guda biyu,shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta)*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 6335.

    iii-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
    *(Yin azumin ranar Arfa,ni ina fatan Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ta biyo bayanta...........)*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3853.

       Allah ne mafi sani.

    *Allah ka bamu ikon aikata wadan nan aiyuka masu albarka ka kuma sadamu da alkhairin wannan rana mai albarka.

    Ina barar adduarku Allah ya gafartawa mahaifina da sauran Musulmai da suka riga mu gidan gaskiya gaba daya mu kuma Allah ya sanya mu cika da Imani idan ta mu ta zo*.

    No comments