Kannywood Sharhi Kan Sabbin Hotunan Da Zainab Indomie Ta Saki Wayanda Suka Dau Hankali Jama,a
Jaruma Zainab Abdullahi kenan wacce akafi sani da (Zainab Indomie).
Daya daga cikin fitattun jarumawan mata da akeji dasu a baya a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood.
Jarumar dai tauraruwanta ta dushe ne yayin data kamu da wata cuta mai sanya jiki ramewa wanda hakan ne ya haifar mata da ramewa sosai mutane da dama basa iya ganeta sakamakon kowa yasanta mai jiki ne kuma Kyakkyawar mace son kowa kin wanda ya rasa.
Bayan kwashe tsowon lokaci ba tare da anji duriyar jarumar ba sai akajiyota lokaci guda tana ikirarin cewa bata cire rai da dawowa bakin aiki ba bayan ta fara samun sauki wannan kalamai nata yasan mutane cece-kuce sakamakon ganin halin da jarumar take ciki.
Kwatsam sai gashi kuma cikin satin nan jarumar ta saki wasu sabbi Hotuna nata wayan da tabawa mutane mamaki sosai domin kuwa Hotunan sunja hankali jama,a sosai a kafafen sada zumunta musamman Instagram da Facebook domin kuwa wayannan kafefe sune sukafi tara jama,a.
Mutane da dama basu gane Jarumar ba sakamakon yadda ta sauya cikin kankanin lokaci hakan ne ya fara sanya wasu suka fara aminta da maganar da jarumar tayi a kwanakin baya na cewa bata cire rai da dawowa bakin aiki ba yanzu dai da yawan mutane sun aminta da cewa ko yanzu zata iya dawowa bakin aiki kuma suna da yakinin tauraruwarta zata iya haskawa kamar yadda ta haska a baya.
Ita daman ai cuta ba,ayota ba sai da Allah yayi maganinta dan haka cire rai da samun lafiya yayin rashi lafiya tamkar cire rai ne da rahamar Ubangiji da haka nake cewa cuta ba mutuwa bace da maganinta! Da maganintaa!!.





No comments