Wasiyyan Wani Uba Ga Yarsa Ana Gobe Aurenta - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Wasiyyan Wani Uba Ga Yarsa Ana Gobe Aurenta


    ABINDA WANI UBA YA FADAWA YARSA ANA GOBE ZA'A SANYATA A LALLE.

    'Yata, gobe zaki daina amsa sunarki na 'yata.  Zakiyi auren farin ciki zaki auri muradin ranki wanda kike qauna.

    Kada kiyi kewata domin na cika burina na aurar dake ga wanda kike qauna, yanxu kuma ya rage naki ki cika naki burin.

    Daga yarintarki, na samu nabaki tarbiya cikin ikon Allah ko?  Kafin ki amsa mini da cewa eh, akwai wani abinda nakeso na fada miki dangane da zama da mijin aure na kasancewarki matar aure.

    Kina tuna lokacin da kika rubuta jarabawar  WAEC da JAMB?  Kinzo kinsameni na baki #20,000 na registration? Dukda cewa nabaki, toh kudin ba nawa bane. Nasan kin dauka cewa ni na biya miki kudin. Maganar gaskiya shine lokacin banida sisi, Mahaifiyarki ita tabani. Tanada damar da zata baki kudin da hannunta, ammana sai ta bani ni na baki.

    Ki zamto mai tallafawa mijinki. Wani lokacin rayuwa takan tsananta, mijinki zai iya zamowa a fusace, domin rayuwa tayimar daurin tamtam, zai iya jin tsoron kada ya rasaki domin abin hannunshi ya kare a wannan lokacin, toh a wannan yanayine yake buqatar tallafinki, ki zamto mai bashi karfin guiwa sosai.

    Babban hanyar da zaki bi wajen nunawa mijinki kina qaunar shi shine kina girmamashi da kuma kuma girmama ra'ayinshi!.

    Ta yiyu kuyi jayayya tsakaninku, ko kuma kiki aminta da ra'ayinshi, ammana a karshen ranar, ki nunamar cewa ya cancanci ki girmamashi. Kina tuna lokacin da nayiwa Mahaifiyarki tsawa? meye tayi lokacin? Shiru tayi

     Kina kuma iya tuna wani lokaci data mini tsawa? Meye nayi? Shiru nayi nima lokacin.

    Yake 'yata, ki zamto mai shiru ga mijinki lokacin da yayi fushi. Lokacin da dayanku zuciyarsa ke tafasa, dayanku ya tabbata xuciyarsa tana sanyaye. Idan ma'aurata biyu dukkansu suna tsawa wa juna a tare, ananne babbar matsalar aure ke somawa.

    Farkon abinda yakamata kisani dangane da mijinki shine abincin dayafi so! Idan sunada yawa, ki tabbata kin riqesu a ranki. Kada kibari sai ya roqa kimar, ki zamto kinayi basai ya nema ba.

    Akwai wani lokacin da Mahaifiyarki ta kamani ina wasa da hannun wata mata, tabbass matar ta janye hankalina ammana bawai ina cheating din mahaifiyarki bane. Lokacin data ganmu, batayi fada da matar ba, kawai Kama hanyar ta tayi ta wuce batace uffanba. A ranar naji tsoron komawa gida domin ina tsoron abinda zan tarar a gidan idan na koma. Ammana sainayi ta mazan na koma gida. Kuma wallahi batace uffanba. Ta hadamin abinci kamar yadda ta saba. A hakan a tsorace nake domin nasan abinda na aikata. Saina fara bata haquri ta kuma ce babu Komai ya wuce. Daga wannan rana ban sakewa yiwa wata mace kallo na biyu ba.

    Waye yasan meye zai faru da tayimin masifa ta balbaleni? Wataqila dana fita na bar mata gidan na koma wajen waccar matar data kamani da ita.

    Wani lokacin shiru kan zamo silar sulhu maimakon fada da masifa da balbalin bala'i.

    Ki manta da wadancaan littatafa na soyayya da kike karantawa lokacin kina budurwarki. Kin tuna wadannan finafinai na soyayya na India da American? Wassu nollywood movies dinnan? Ki manta dasu, kada ki tsammanin rayuwar aurenki yazamto irin wadancaan.

    Rayuwa a zahiri ba kamar Wacce wassu directors da marubuta, su artist da producers suka rubuta bane, rayuwar aure Allahu Jalla wa Azza Ne ya ke directing kuma Shine producer, Shine Artist

    Abu na karshe dana buqata kisani shine....... Kina tuna lokacin da aka haifeki?

    Bayan aure na da Mahaifiyarki, rayuwa ta tsananta garemu. Mamarki ayyuka biyu takeyi domin ta tallafa mana, bawai bana aiki bane, nima ma'aikaci ne. Ina dawowa gida karfe 6 na yamma, ita kuma karfe 8 na yamma kuma a gajiye. A hakan bata ta6a hanani abinci dare ba ko kuma kin kulawa da wajen kwanciyar mu. A hakan aka samu aka haifeki cikin ikon Allah.

    Kada ki kuskura ki hana mijinki kanki ko abinci Komai gajiyanki, ki zamto mace tagari

    Har abada kinanan a yar daddy.

    No comments