Wani Attajirin Mai Kudi Ya Dauki Nauyin Auren Yan Mata Guda 100 A Sokoto - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Wani Attajirin Mai Kudi Ya Dauki Nauyin Auren Yan Mata Guda 100 A Sokoto


    Wani Attajiri A Jihar Sakkwato Umarun Kwabbo, Zai Dauki Nauyin Auren Mata 100.

    Wani attajiri mai taimakon jama'a da ke jihar Sakkwato mai suna Alhaji Umaru Kwabbo AA, ya bayyana aniyarsa ta daukar nauyin aurar da gwagware da 'yam mata 100 da ke jihar.

    Umarun Kwabbo ya bayyana hakan ne yayin wani taron addu'o'i da aka gudanar a gidansa da ke Sakkwato, inda ya bayyana aniyarsa ta taimakawa wajen rage yawaitar mata zawarawa da 'yan mata da  ke zaune babu  mijin aure.

    Umarun Kwabbo wanda kuma har wa yau shi ne Jarman Sakkwato, ya yi alkawarin daukar nauyin duk wasu abubuwan bukatu na aure da wadanda za a yi wa auren za su bukata.

    Abubuwan da suka hada da biyan sadaki, kayan lefe, kayan daki da kuma wasu muhimman kyaututtuka da zai a bai wa sabbin ma'auratan.

    Ya ce, wannan nauyi ne da ya dade yana son Ya dauka, domin sakantawa al'umma, da yin koyi da tarbiyyar addinin Musulunci, tare da  kuma tallafawa maza da mata da ke bukatar yin aure amma rashin kudi ya hana.

    A jawabin sa, tsohon sakataren gwamnatin jihar Sakkwato, Alhaji Muhammad Maigari Dingyadi, ya yabawa Alhaji Umarun Kwabbo bisa wannan kyakkyawar aniya tasa ta tallafawa al'umma a jihar.

    Taron ya samu halartar manyan malamai, manyan 'yan kasuwa da 'yan siyasa.

    No comments