Kannywood Ali Nuhu Ya Goyi Bayan Kungiyar ONE Mai Karajin Kare Lafiyar Al'umma
Mata 210,000 suka mutu sanadiyar tabarbarewar fannin cikin shekara
Fitaccen jarumi Ali Nuhu ya goyi bayan kungiyar ONE wajen yaki tare da yin kira da babban murna domin ganin an samad da tabbatacciyar cibiyoyin kiwon lafiya a yankuna daban daban na fadi kasa.
Ziyarar da Jarumin ya kai tare da kungiyar ONE yankin Kantudu dake nan jihar Kano ba'a samu labari mai dadin ji.Al'ummar Kantudu na fama da rashin Likita da karancin magunguna kana da shanu ake garzaya da mara lafiya cikin gaggawa yayin da rashin lafiya ya taso.
Ali Nuhu tare da jami'an ONE sunyi shaida game da matsalloli da ake fuskanta a kasar na koma baya a bangaren kiwon lafiya.
A nan cibiyar kiwon lafiya dake kantudu wanda ita kadai ne a yankin ana fuskantar rashin kayan aiki da ma'aikata da magunguna kuma iyaye mata da yara kanana ke kan gaba wajen fama da illar da rashin haka ke haifarwa.
A bidiyon wanda ke nan kasa, al'ummar yankin sun koka game da wannan matsalar da suke fuskanta ciki hare da mai garin kantudu wanda ya bada kisan yadda wata mata ta mutu sanadiyar rashin motar agaji mai tafiya da mara lafiya cibiyar kiwon lafiya.
Bisa ga kundin tsarin dokar kasa a sashen dokar kiwon lafiya ta 2014, duk wani dan kasa yana da damar samun kulawa daga hukumomin kiwon lafiya.
Rashin wanan damar zai sanya a samu mutuwar mata masu juna biyu yayin da suke neman haihuwa kana wasu kuma zasu kamu da cututuka kamar ciwon suga. Hakazalika rashin haka zai sanya a samu agajin magani na gaggawa ga raununuka da ake samu sanadiyar hatsarurruka dake faruwa a hanyoyi.
Jagoran ONE ta Nijeriya Serah Makka-Ugbade a cikin wata takarda da aka fitar a garin Abuja tana cewa: "Fanin kiwon lafiya a nijeriya yana fama da matsaloli. Kuma har yanzu ba'a gan canji mai nuna cigaba ko inganta fannin ga yan kasar. Fannin tabarbarewa kawai yake yi. Shin har zuwa yaushe zamu cigaba da samun haka a fannin?. Lokaci yayi da zamu tashi tsaye wajen canja haka. Lokaci yayi da duk wani dan Nijeriya zai samu damar duk wani tsarin neman magani gorgodon karfin su."
No comments