Gasar Hikayata Ta BBC Saura Awa Biyu A Rufe Na Shiga
BILKISU SANI MAKARANTA ce ta zama gwarzuwar gasar Hikayata ta biyu a 2017, gasar da sashen Hausa na BBC ya ke shiryawa duk shekara. Ga yadda su ka yi da wakiliyarmu JAMILA UMAR TANKO:
Za mu so mu ji takaitataccen tarihinki?
An haife ni a garin Gusau. Na yi makarantar firamare a Gusau, na yi sakadire a FGGC Gusau. Daga nan na wuce FCE (Technical) Gusau. Na shiga jami’ar Bayero ta Kano, inda na yi karatuttuka daban-daban. Yanzu haka ina matsayin mataimakiyar shugabar makaranta a school for countinue education (Women)
Da ma can ke marubuciya ce?
Eh, na taba rubuta labari daya, kuma na buga shi ya shiga kasuwa. Sunansa ‘Allah Mai Lokaci’.
Yaya a ka yi ki ka shiga gasar Hikayata?
Farko da a ke tallata gasar na yi niyyar shiga, amma ban samu na shiga ba sai a kurarran lokaci. A na saura kwanaki biyu a rufe na fara rubutun labarin. Bai fi sauran awanni biyu a rufe ba, sannan na samu damar turawa, saboda rashin kyauwun yanayi. Har da kamar ma zan fasa.
Wanne farin ciki ki ka ji lokacin da a ka ce kin sami nasarar zuwa ta biyu?
Alhamdulillah! Na yi farin ciki, don ban yi tsammani ba.
Wanne kira za ki yiwa mata?
Duk wacce ta ke da sha’awar shiga gasa, kar ta yi kasa a gwiwa; ta shiga a fafata da ita. Mai tsoro ba ya zama gwani.
Menene burinki nan gaba a kan rubutu kasancewar da ma ke ma marubuciya ce?
Burina na yi rubutu mai ma’ana, wanda zai amfani al’ummata.
Akwai waxanda ki ke son mika godiya a gare su?
Ina mika godiya ga gidan radiyon BBC sashen Hausa. Godiya ga mai gidana, Dr. Hamza Muhammad da uwar xakina a rubutu, Sa’adatu Baba Ahmad.
No comments