Falalar Dake Cikin Lokacin Sanyi
YANAYIN SANYI AKWAI DADI SOSAI.
A wannan yanayi na sanyi da mutum zai duba yanmatan arewa da sauran matan aure marasa yin decent dress wato shiga irinta kamaka, zakaga sun koma dressing decently ba don Allah ba sai don tsoron sanyi.
Zakaga mata da bunjumemen hijabi, ga niqab ga socks hannu da kafa duk sun jefar da wassu leggings wassu gyalulluka tayani gantali, wassu hills, wani yawan sanya eye shadows da shafe-shafen caro-white da dai sauransu.
Inama ace yadda mata ke dressing yanxu zasuci gaba dayin hakan koda bayan sanyi ya wuce?
Wallahi da tabbass ansamu raguwar aikata 6arna a doron kasa.
Abdullahi bn Mas'ud Rabiyallahu Ta'ala anhu yana cewa:
مرحبا بالشتاء تتنزل فيه البركة، ويطول فيه الليل للقيام، ةيقصر فيه النهار للصيام
Maraba da lokacin sanyi, albarka tana sauqa, dare yana tsawaita domin sallar dare, yini yana gajarta domin Azumi.
Yan'uwa masu hankali idan sanyi yazo tashi ake yi tsaye a nemi Aljannah, saboda saukin Ibada. Bawai lokacine da mutum zai nemo room heater da wassu electric blanket ba ko kaskon wuta ya sanya a daki, lokacine na tashi a nemi gafara a wajen Mai gafarar
Sannan zamu ga cewa dare yana tsawaita saboda mutum ya tashi yayi ta Ibadah irinsu tahajjud, karatun Qur'ani, ammana ba kowane yake iya daurewa ya tashi cikin wannan yanayi na sanyi ba sai wanda Allahu Azza wa Jalla Ya za6a.
Sannan kuma yini yana gajarcewa saboda masu azumi, sannan kuma babu zafin Rana da zata sanya mai azumi ya wahalta. Kuma nan-da-nan sai ka ga an sha ruwa domin wani yanayi da turawa ke kira: "short day long night".
Magabata na kwarai suna murna da farin ciki idan aka ce wannan lokaci yayi. Kuma suna kokari wurin ganin sun sami abinda suka samu na lada kafin lokacin ya tafi.
Yaku Gayun zamani, wannan yanayi ba lokacine na shan wiwi ba. Domin nakanga wajen sayarda tabar wiwi yafi cika a duk lokacin da akace anfara busa sanyi. Wallahi Gayu har layi sukeyi wajen sayan tabar wiwi. Ku daina shan ganye babu kyau gayu.
Sannan kuma Gayu ku sani ba lokacine na tapping current ba kamar yadda kuke fadi. Don menene, yawancin lokuta indai akace sanyi ya busa toh tabbass akan samu matsala da Gayu wajen hira domin idan ba'a maida hankali ba yanxu Gaye zai nemi ya shigewa mace cikin hijabinta su zama su biyu wai da sunan ta 6oyeshi kada yaji sanyi. Inace ba ke kika aifeshi ba? Toh da zarar Gaye yace miki wallahi yafara jin sanyi, toh yi maza ki cemar a gaida su Goggo.
Don haka sai mu dage wurin Ibaada da kuma ci gaba da yin dressing decently daga yanxu har sanyi ta wuce.
Allah Kabamu Ikon yin ibaada a wannan lokaci na sanyi Ka kuma sadar damu da alherin dake tattare dashi, akasin hakan kuma Ya Allah Ka kawar mana dashi.
No comments