Facebook Yayi Sanadiyar Daure Wasu Dagarun Soji A Gidan Yari
Wata kotun soji ta daure wasu dakarun Majalisar Dinkin Duniya biyu masu aikin tabbatar da tsaro a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka saboda amfani da Facebook.
An same su da laifin kulla zumunta da wata mata a shafin Facebook inda suka yi ta tura wa wata mata hotunan bidiyo, ita kuma ta sanya hotunan a Facebook tare da rubuta bayanan batanci game da sojoji.
Hakan ya sa an tuhumi dakarun da saba wa dokar aiki da nuna rashin ladabi.
Bayan aikin tabbatar da tsaro na tsawon kusan shekaru biyu da dakarun MDD din 'yan asalin Kamaru suka yi a Jamhuriyar tsakiyar Afrika, a yanzu kuma za su yi zaman gidan yari na soji a birnin Yaounde.
Daya daga cikin dakarun ya bayar da tabbacin cewa a watan Agusta na shekarar 2013 a lokacin da yake aikin tabbatar da tsaro a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, ya samu gayyatar wata mata a shafinsa na Facebook inda ta neme shi da su kulla abota.
Daga bisani dai sai ya amince mata.
Amma bayan haka sai ya aika mata da wasikar gayyata don ganawa da ita ke-ke-da-ke-ke inda ita kuma ba ta amsa bukatar ba.
Daga baya ne sai matar ta fara wallafa wasu hotuna da kuma bayanai masu barazanar tayar da hankali a kan tawagar dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.
Watanni biyu bayan dawowarsa daga wannan aiki, kawai sai aka aika masa sammaci domin ya bayar da wasu bayanai game da tuhumarsa da ake yi da kulla hulda da wata mata game da sakon hotunan bidiyon da ya dinga aika mata.
Sojan dai ya amsa cewa sun dinga yin musayar hotunan bidiyo a tsakaninsu tare da takwaran aikinsa da suke tsare a yanzu haka.
Amma kuma ya yi mamaki da kuma nuna shakku game da mutumin da ya sanya hotunan bidiyon da suka jefa shi a cikin wani hali.
Babban lauyan Gwamnati kuma ya ce takwaran aikin soja na farko da aka tsare su tare yana da shafukan Facebook hudu daban-daban, inda kuma yake amfani da sunaye daban-daban.
Sai dai sojan ya musanta zargin.
Babban lauyan na gwamnati ya ce haka ne ya kai ga yanke wa mutumin hukunci mai tsanani.
An bai wa sojojin zuwa ranar 9 ga watan Disamba domin daukaka kara.
Source By Bbchausa
Source By Bbchausa
No comments