Dan Sarkin Saudiya Ya Siya Gida Mafi Tsada A Duniya
Ana Zargin Yariman kasar Saudia da Siyan Gida Mafi Tsada A DuniyaDaga Ahmadu Manaja BauchiJaridar New York Times ta Amurka, ta rawaito cewa Yarima mai jiran gado a Saudi Arabia, Mohammed Bin Salman, shi ne ya sayi wani gida na alfarma a boye a kasar Faransa.
Jaridar ta ce, takardun cinikin gidan da akayi a shekarar 2015, an gano cewa shi ya sayi gidan ta hanyar amfani da wasu dumbin kamfanoni da aka yiwa rijista.
Gidan wanda ke dab da fadar shugaban kasar Faransa, yana da wurin ajiyar giya na karkashin kasa da sinima da korama da kifaye masu alfarma nau'in koi da sturgeon da kuma wurin shakatawa na alfarma da ke karkashin kasa.
Kudin gidan dai ya kai dala miliyan 320, wanda mujallar Fortune ta kira shi da gidan da ya fi sauran gidaje tsada a duniya.Mai magana da yawun ofishin jakadancin S
audia a Amurka, ta zargi ma'aikatan jaridar da yin rahoto son rai.
A watannin baya-bayan nan, Yarima Mohammed, yajagoranci yaki da cin hanci da rashawa da cin amanar kasa da kuma yadda ake nuna wa wasu gata a kasarsa.
A shekarar 2015, an rawaito cewa, Yariman ya sayi wani jirgin ruwa na alfarma daga wajen wani hamshakin dan kasuwa a Rasha a kan kudi dala miliyan 590.Kazalika jaridar ta New York Times, ta rawaito cewa shi ne kuma ya sayi wani zane na Salvator Mundi wanda Leonardo da Vinci ya yi a kan kudi dala miliyan 450.
No comments