An Karrama Shugaban Izala A Kasar Spain
An Karrama Shugabannin IZALA A Kasar Spain.
Kungiyar Wa'azin Musulunci ta Sautus Sunnah Europe mai rassa a kasashen Turai, ta karrama shugaban kungiyar jama'atu Izalatil bidah wa ikamatissunnah Sheikh Abdullah Bala Lau da Babban Sakataren kungiyar Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe da shaidar (Certificate) na girmamawa Saboda gagarumar nasarorin da suka samu na da'awa da yada Sunnah wanda suka dauki kusan makwanni biyu suna yi a kasashen turai.
Kungiyar mai wa'azin Musulunci ta Sautus sunnah Europe ta karrama Maluman ne a babban Masallacin Juma'a na Masjidul Huda dake birnin Barcelona a Kasar Spain a ranar Laraba bayan kammala Muhadharah wacce manyan Maluman suka gabatar.
Masoya daga cikin masallacin sun yi cuncirindo suna ta kabbara yayin da ake karrama malamansu.
Allah ya Kara daukaka Malaman Sunnah, ya bada Nasarar Da'awa.
No comments