Shugaban Karamar Hukuma Ya Wanke Knsilarsa Da Mari - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Shugaban Karamar Hukuma Ya Wanke Knsilarsa Da Mari


    Shugaban Karamar Hukuma Ya Sharara Wa Wata Kansila Mari A Jihar Kebbi

    Daga Muawiya Abubakar Zurmee

    A jihar Kebbi wata kansilar mai sunan Honarabul Rakiyya Musa Birnin Tudu ta ce shugaban karamar hukumar ta Fakai ya mare ta har sau biyu saboda ta ba shi shawarar ya rika tafiya tare da kansilolinsa kuma ya biya ma'akatan karamar hukumar albashin watanni hudu da suke binsa.

    Rakiya Musa Birnin Tudu, wadda kansila ce mai wakiltar mazabar Birnin Tudu a karamar hukumar, ta ce sau biyu Alhaji Musa Rabi'u Jarma yana marinta.

    Rakiya ta ce daga cikin korafin da jama'ar karamar hukumar ke yi akwai batun albashi, inda ake kwashe watanni ba a biya wasu albashinsu ba, wasu kuwa ba gaira ba dalili aka rage musu albashi.

    Don haka ne ta bayar da shawarar cewa ya kamata a gyara, saboda su kansiloli su suka fi kusanci da jama'a, su ake yi wa korafin.

    "Bayan na gama bayanina ne, sai shugaban hukumar ya harzuka, wai don na ce ya rungumi komai shi kadai baya sanya kowa a harkokin tafiyar da karamar hukumar, hakan ya sa ma'aikata da dama ba sa zuwa ma aiki ciki har da daraktoci," in ji ta.

    Kansilar ta ci gaba da cewa bayan ya harzukan ne, sai ya tashi daga kujerarsa ita kuma kanta na duke, ba ta yi aune ba kawai sai ta ji an wanka mata mari har sau biyu.

    Rakiya ta kara da cewa, "Sai shugaban karamar hukumar ya ka da baki ya ce mini ba a taba marin kansila ba a tarihin karamar hukumar, to yau shi ya mara kuma ya mari banza, don haka duk wanda zan fadawa na je na fada sai kawai ya fice daga wajen taron".

    A cewarta, bayan ya mare ta sai ta zabura ta tashi ta tambaye shi "me na yi maka daga fadin gaskiya don a yi gyara?"

    A yanzu haka dai wannan batu yana hannun gwamnatin jihar da kuma jam'iyyar APC mai mulki, inda mutane ke sa ido don ganin matakin da za su dauka.

    No comments