Gomnatin Shugaban Kasa Muhammad Buhari Zata Karawa Ma'aikata Albashi
Gwamnati Za Ta Fara Zama Kan Batun Karin Albashi Ga Ma'aikata.
Ministan Kwadago, Chris Ngige ya tabbatar da cewa a ranar Litinin mai zuwa ne, Shugaba Buhari zai kaddamar da kwamitin mutane talatin wanda zai duba yadda za a karawa ma'aikatan gwamnati albashi.
Kwamitin wanda Misis Amal Pepple za ta jagoranta, ya kunshi ministocin Kwadago, Kudi, kasafin kudi, Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya sai kuma gwamnonin jihohin, Osun, Imo, Gombe, Kebbi da Filato wadanda za su wakilci sauran jihohi. Sai kuma kungiyoyin Kwadago daban daban.

No comments